1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhimmancin alakar Jamus da Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari YB
May 2, 2019

A ziyarar da take yi a wasu kasashe na yankin Sahel, a ranar Alhamis ne Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke isa birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar. 'Yan Nijar dai sun bambamta a kallon huldar ta Jamus da Nijar.

https://p.dw.com/p/3Hoih
Niger Besuch Angela Merkel mit Präsident Mahamadou Issoufou in Niamey
Hoto: DW/S. Boukari

Daga cikin manyan batutuwan da ake ganin Angela Merkel din za ta tattauna a kansu da shugaban kasar ta Nijar Mahamadou Issoufou akwai abin da ya shafi tsaro, da ma inda aka kwana ga batun kwararar bakin haure masu kokarin shiga Turai ta barauniyar hanya. 

Kalla Ankouraou shi ne ministan harkokin wajen kasar ta Nijar ya yi waiwaye adon tafiya kan huldar kasashen biyu inda ya ce tun 1961 hulda ke wakana tsakanin Nijar da Jamus inda ta kama wa kasar kan harkoki na lafiya da samar da abinci da ma batu na tsaro.

Sai dai batun da ke daukar hankali a wannan ziyara ta shugabar gwamnatin Jamus shi ne na tsaro ganin yadda kasar ta Nijar ke tsakiyar kasashen da ake tashe-tashen hankula da kuma kasancewar dakarun sojojin kasar ta Jamus da ke cikin kasar Nijar, ko da yake akasarin ayyukansu suna yi ne a can kasar Mali. Moussa Aksar dan jarida ne mai bincike, kuma na bin diddigin yadda sojojin kasashen waje ke gudanar da ayyukansu a Nijar ya ce sojan na Jamus na kokari wajen ba da horo ga sojojin na Nijar.

Von der Leyen reist nach Niger
Ursula Von der Leyen ministar tsaron Jamus a lokacin wata karbar gaisuwar sojan Nijar a 2017Hoto: Picture-alliance/dpa/B. Pedersen

Da dama dai na yaba yadda kasar ta Jamus ke gudanar da huldarta da kasar ta Nijar, musamman ma a fannin raya karkara, sai dai kuma kan batun jibge sojojin kasashen waje duk da yabawa, kokarin na Jamus kan Nijar a cewar Nouhou Mahamadou Arzika na kungiyoyin fararan hula masu adawa da kafa sansanonin sojoji na waje, Jamus na kokokari a Nijar sai dai babu bukatar a mayar da Nijar tamkar baiwa.

A wata hira da aka yi da shi a Jaridar Die Welt ta kasar Jamus, ministan cikin gida na Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed kuma dan takarar jam’iyya mai mulki a zabe mai zuwa, ya ce ganin irin kokarin da suka yi na yaki da kwararar bakin haure, lalle Jamus da sauran kasashe sun yi kokari, amma ba kokari ne da ya taka kara ya karya ba daga cikin abubuwan da suka jira daga kasar ta Jamus.