Afirka ta dauki hankalin taron G20 | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 09.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka ta dauki hankalin taron G20

Kasashen Afirka sun shiga sahun gaba a taron rukunin kasashen G20 masu karfin arzikin masana'antu da Jamus za ta dauki nauyi.

Jaridar Süddeutsche Zeitung, a sharhin da ta yi mai lakabi da tallafin Jamus ga Afirka a jagorancinta na rukunin kasashe 20 masu ci-gaban masana'antu.

Jaridar ta ce hadakar rukunin kasashe 20 masu cigaban masana'antu na duniya tare da kasashe masu kasashe da tattalin arzikinsu ke tasowa na da sha'awar ganin sun taimakawa Afirka zama da gindinta.

A kan haka ne ministocin kasashen 20 masu ci-gaban masana'antu suka kafa wani shirin tuntuba da Afirka wanda aka yi wa lakabi da "Compact with Africa" a turance, wannan shiri wanda zai gudana karkashin jagorancin Jamus a shugabancin karba-karba na kungiyar zai bunkasa raya tattalin arziki da karfafa dankon dangantaka da nahiyar ta Afirka. Ana sa ran kasashen na Afirka su taka rawar gani a taron kolin G20 da zai gudana a birnin Hamburg a watan Yuli mai zuwa.

Rukunin kasashen masu cigaban masana'antu musamman ma turai sun nuna karin sha'awa akan Afirka ne saboda fargabar da suke da ita game da karuwar kwararar yan gudun hijira da ke ta tekun Baharum zuwa nahiyar turan wanda ke kara yin kamari tun daga shekarar 2008.

A cewar jaridar, kungiyar ta G20 ta fahimci taimakon raya kasa kadai ba zai wadatar ba, akwai bukatar zuwa jari domin taimakawa kafuwar hukumomi da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar a nahiyar. Wanda hukumomi kamar bankin duniyaa da bankin zuba jari da kasashen turai EIB za su iya tallafawa.

Bugu da kari jaridar ta Süddeutsche Zeitun ta ce wani abu mai muhimmanci shi ne cudanni in cudeka ta fuskar kasuwanci tsakanin kasashen Turai da Afirka.

Yayin da Afirka ka iya zama babbar kasuwa ga kayayyakin turai a waje guda kuma Afirka za ta ci gajiyar kawancen tattalin arziki da cinikayya da kuma fasaha daga kasashen na Turai.

Jaridar Welt am Sonntag ta yi sharhi kan tasar mutane miliyan 21 a unguwar marasa galihu da hukumomin jihar Lagos a Najeriya suka yi domin samun aiwatar da shirin gina sabuwar alkarya ta Megacity.

Lagos da ke zama birni mafi girma a Afirka yana karfin tattalin arziki fiye da kasashen Kenya ko Cote d'Ivoire ko kuma Ghana. Kasashe shida ne dai a duniya suka fi saurin bunkasa da karuwar yawan al'umma 700,000 a kowace shekara. Birane kamar Johannesburg da Nairobi da Daressalam da Khartoum da kuma Casablanca za su haura yawan mazauna milyan goma idan tafiya ta yi tafiya. Jaridar ta yi nuni da cewa yawan al'ummar Afirka na bunkasa fiye da kowane yanki a duniya.

Birnin Lagos dai na daukar kansa a matsayin ja gaba wajen magance kalubalen da yan al'ummar ke kawowa ta la'akari da cigaban da ya samu cikin shekaru goma da suka wuce.

Jaridar ta ce a yan shekaru da suka wuce birnin ya yi kaurin suna da tulin shara a kan tituna amma a yanzu ya zama tarihi.

Ita kuwa jaridar Der Spiegel a sharhinta mai taken shekaru 20 bayan faduwar gwamnatin Mobutu rudani na cigaba da wakana a kasar.

Jaridar ta yi tsokaci da yadda Joseph Kabila ya maye gurbin mahaifinsa da salo na kama karya a JamhuriyarDimokradiyyar Kongo.

Ta ce bayan wa'adin mulki sau biyu har yanzu shugaban yana kokarin cigaba da damfarewa a kan karagar mulki.

Shugaban dai ya yi watsi da dukkan zarge zargen da yan adawa ke masa yana mai cewa basu da tushe balle makama.