1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Mafita a rikicin Afghanistan

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 3, 2019

Ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer ta shawarci mahukuntan Afghanistan su zauna kan teburin tattaunawa da 'yan kungiyar Taliban da ke da tsatsauran ra'ayin addinin Islama.

https://p.dw.com/p/3U96x
Afghanistan l Verteidigungsministerin Kramp-Karrenbauer trifft Präsident Ghani
Ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer da shugaban Afghanistan Ashraf GhaniHoto: picture-alliance/dpa/R. Gul

Annegret Kramp-Karrenbauer ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ta gudanar da Shugaba Ashraf Ghani na Afhghanistan din yayin wata ziyara da ta kai Kabul fadar gwamnatin kasar, inda ta ce ta ma tattauna da Ghani kan batun na sulhu. Ministar tsaron ta Jamus ta kuma kai ziyara ga sojojin kasarta da ke Afghanistan din. An dai yi ta sukan Amirka bisa zama kan teburin sulhu da ta yi da 'yan Taliban din kai tsaye, ba tare da sanya mahukuntan kasar cikin tattaunawar ba.