Abu Namu: Sabunta kayan kicin lokacin azumin Ramadan | Zamantakewa | DW | 13.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Abu Namu: Sabunta kayan kicin lokacin azumin Ramadan

A lokacin azumin watan Ramadan mata musamman Hausawa na ba da kokari wajen sabunta kayan girke-girke da na kicin.

Shirin ya yi nazari ne kan wata al'ada da mata musamman na Hausawa ke yi a duk lokacin azumi, ta yadda za ka ga mace ta sauya kwanuka da kayan kicin musamman ma kwanukan mai gida. Wasu matan kan shiga adashi su sayi wadannan kwanukan, sai dai ba kowanne namijin ne ke yaba da wannan kokari na matan ba, haka kuma wasu matan kan takura mazajensu ne domin samun kudin sabunta kayan.

Shirin ya yi karin haske kan dalilan da ya sanya matan ke yin wannan al'ada ta sauya kayan kicin lokacin azumi.

Sauti da bidiyo akan labarin