A Kamaru mutane na taimakon sojoji da jini | Zamantakewa | DW | 19.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

A Kamaru mutane na taimakon sojoji da jini

'Yan Kamaru sun amsa kiran bayar da agajin jini ga sojojin da ke yaki da kungiyar Boko Haram da kuma 'yan tawaye a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika.

Sai dai likitoci a kasar na bayyana fargabar samun masu dauke da cutar HIV a cikin masu bayar da jinin. An samu dandazon matasa a cibiyar wasanni ta birnin Yawunde domin bayar da taimakon jini kyauta ga sojojin da suke yaki da kungiyar Boko Haram, sakamakon yadda sojojin kasar da yawan gaske da suke a kasashe makwabta domin yaki da ayyukan ta'addanci, wadanda su sun samu raunuka ba ma kawai a yaki da 'yan Boko Haram ba har ma da rikice-rikicen da suke afkuwa a yankin gabashin Jamhuriyar Kamarun.

Fadimatu Iyawa mai shekaru 18 na daya daga cikin masu son bayar da jinin ga rundunar sojojin, inda ta ce ta yi hakan da zummar karawa sojojin kwarin gwiwar daukar mata fansa sakamakon kashe mata ukku daga cikin 'yan uwanta yayin wani harin kunar bakin wake da ya gudana a yankin arewacin Kamarun.

Wani Malamin makaranta Neba Joel mai shekaru 32 yace ya zo bayar da jinin ne domin nuna goyan baya da kishin kasa ga sojojin.

Mutane da dama suka fito kwansu da kwarkwatarsu saboda bayar da taimakon, Lionnel Koungaba wanda ke zama babban jami'i a majalisar matasan kasar wanda kuma shi ne ya hada gangamin matasan yayin bayar da jinin, ya ce matasa sun masa kira.

Sai dai wani likita Dr Ndansi Elvis da ke karbar jinin ya ce inda gizo ke sakar shi ne wasu daga cikin mutanen da suka bayar da jinin sun kamu da cututtukan da suke iya yaduwa, wanda kuma yana da hadarin gaske, al´amarin da ministan lafiya Andre Mama Founda ke cewar ana bukatar roba dubu dari hudu ta jinin, wanda hakan ya zama wani babban kalubalen da ya sanya karancin jinin da a wasu lokutan kan tilasta ma'aikatan lafiya bayar da jininsu da zarar an samu aikin da ke bukatar taimakon gaggawa.

Sojojin Kamaru dubu uku ke fafatawa da kungiyar Boko Haram, a makon da ya gabata sai da Kamarun ta yi alkawarin bayar da sojoji sama da dubu biyu ga rundunar hadin gwiwar fatattakar Boko Haram da ke da mazauni a kasar Chadi.