Ziyarar Jonathan a Kano na cike da kace-nace | Siyasa | DW | 15.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Jonathan a Kano na cike da kace-nace

Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya gudanar da gangamin karbar tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau a jam'iyyar PDP mai mulki. Sai dai masu fashin baki suka ce ya saba wa dokokin zaben kasar.

Tun cikin watan Janairun da ya gabata ne tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ya ayyana sauyin sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP mai mulkin Najeriya, bayan da ya ce akwai alamun rashin adalci a sabuwar jam'iyyar. Wannan dai shi ne ummul- aba'isan wannan ziyara da shugaba Goodluck Jonathan ya kai Kano domin gangamin karbar Shekarau da mukarrabansa, da nufin yi musu lale da marhabin zuwa jam'iyyar PDP.

Nigeria Oppositionspartei APC

Shekarau ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Shugaba Jonathan dai ya yi gayyar mutane domin wannan gangami wadanda suka hada da mataimakinsa Namadi Sambo da shugaban majalisar dattijai David Mark da gwamnonin PDP da suma suka rufa wa shugaban baya domin kara armashin wannan gangami.

Sai dai kuma mutane da dama na ganin cewa gangamin ya saba wa kundin dokokin zaben tarayyar ta Najeriya. Abbati Bako, tsohon sakatare a hukumar zabe ta jihar Kano na daga cikin masu wannan da'awa. Shi ma Eng Magaji Da'u Aliyu da ke fashin baki kan al' amuran yau da kullum ya ce bai kyautu a rinka bikin yada manufar jam'iyya ba, daidai lokacin da ake asarar rayukan mutane a sassa daban daban na kasar.

Nigeria Regierungspartei PDP

PDP mai mulki na zawarcin kuri'u a Kano

Ko ma dai menene an gabatar da wannan taro cikin yanayi na tsauraran matakan tsaro,domin tun a ranar Litinin aka rinka yin arba da sabbin jami'an tsaro dauke da makamai,baya ga sanarwar da jami'an suka yi a kafafen yada labarai na gargadin mutane da su kiyayi halatar wurin taron da ko da sanda balle makami.

Mawallafi: Nasir Salisu Zango daga Kano
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin