Ibrahim Shekarau shi ne mutum na farko da ya mulki jihar Kano da ke arewacin Najeriya tsawon wa'adi biyu a jere karkashin jam'iyyar adawa ta ANPP a wancan lokacin.
Ya yi gwamna ne tsakanin shekarun 2003 zuwa 2011. Bayan da ya bar mulki ya ci gaba da harkokinsa na siyasa har ma daga baya ya kasance ministan ilimi a karshen gwamnatin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.