Najeriya ta raba lambobin girmamawa | Siyasa | DW | 29.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya ta raba lambobin girmamawa

Gwamnatin Najeriya ta karrama wasu 'ya'yanta sama da 300 duk da halin rudani da rashin tabbacin tsaro da ma talaucin da ke addabar mafi rinjayen al'ummar kasar.

Manyan hafsoshin da suka kwashe shekaru har biyar suna gwagwarmaya da masu kokarin haramta karatun boko ko ta halin kaka ne dai suka kai ga lashe gasar tare da samun lamba mafi girma ta kwamandoji na tarayyar kasar ta Najeriya.

Irin wannan lambobin yabon kusan 5,000 ne dai kasar ta kai ga raba wa 'ya'ya da ma bakinta cikin sama da shekaru 50 na tarihin lambar, da sannu a hankali ake yi wa kallon sauyi daga kokari na yabawa bajimta da kwazon kishin kasa, ya zuwa sakawa abokai dama abokan harka.

Kyautar ta bana da aka kai ga raba ta tsakanin 'yan kasar 318 dai na zuwa ne kasa da awowi 48 da bikin kasar na 'yancin kai na shekaru 54, bikin kuma da ke zuwa tsakanin 'yan kasar cikin yanayi na tunanin tana kara baki da rashin tabbas na makoma ga tarrayar Najeriyar, da sannu a hankali ta kai ga sauya wa daga giwa ya zuwa 'yar kyanwa a nahiyar Afurka.

Tuni dai masharhantar kasar ke kallon bata lokaci dama rashin sanin alkibla ga kasar da ke cikin yaki yanzu, amma kuma ke ta bureden yabawa abokan da suka kama hanyar kai wa kasau.

To sai dai kuma a fadar shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan har ya zuwa yanzu fa kyautar na nuna irin rawa dama banbancin da ke akwai tsakanin masu ita da kuma ragowar 'yan kasar da ke kallo daga gefe.

Nigeria Auszeichnungen Präsident Goodluck Jonathan

Daga hagu Onuh Machiel me dafa abinci a fadar shugaban kasa , Imeh Osuah direban tasi da Copral Solomon Dauda

Mafi daukar hankali a kokarin tabbatar da tsoffafi na dabi'un, a bana dai na zaman wani direban (Taxi) da ya tsinci naira miliyan 18 ya maida ta ga fasinjan da ya dauka, da kuma kukun da ya yi hidima a fadar shugaban kasar tun daga shugaba Shagari har ya zuwa shi kansa Jonathan.

To sai dai kuma har yanzu akwai murna da tunani na daukaka ga wasu a cikin wadanda su kai nasarar samun kyautar a bana. Kuma afadar barrister Hassan Liman da ke zaman wani lauyan da aka ba shi lambar da na tarrayar kasar, wai dama ce ta karin damara a taimakon al'umma.

“Wannan kyautar na nufin kasata ta yaba da irin aiyyuka da kishi da kokari da nake nuna mata, kuma sauyin da za ta haifar a gare ni shi ne karin kaimi da sadaukar da kai na aiyyuka da mutum yake yi wa 'yan kasar sa sosai”

Haka shima tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau da yai sauyin sheka daga APC ya zuwa PDP dai, wai lambar kwamandan kogin kwara da ya samu na zaman sabon gwaji ga kokari dama hazakar da yake nunawa.

“Wani zaburarwa ne na cewar an gano kana ba da wata guddummawa a fannoni daban-daban na rayuwa, wannan karin kalubale ne, ina murna kuma ina wa shugaban kasa godiya da karin martabawa da aka bani”

Sauti da bidiyo akan labarin