Zimbabuwe: An jaddada bukatar cire takunkumin Turai | Labarai | DW | 14.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zimbabuwe: An jaddada bukatar cire takunkumin Turai

Sabon shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya yi kira ga kasashen yammacin Turai da su cire takunkumin da ke kan gwamnatinsa, a wani jawabi da ya yi wa jami'an jam'iyyar da ke mulki.

A watan da ya gabata ne dai Mnangagwa mai shekaru 75 da haihuwa ya dare kujerar jagorancin Zimbabuwe bayan da sojojin kasar da jam'iyyar ZANU-PF mai mulki suka juyawa tsohon shugaba Robert Mugabe baya, bayan shekaru 37 ya na mulki.

A shekara ta 2014 Kungiyar Tarayyar Turai ta cirewa jami'an ZANU-PF da wasu kamfanoni da sojojin kasar takunkumin tafiye tafiye, sai dai Amurka ta cigaba da nata haramcin a bangaren tattali da tafiye-tafiye a kan akasarin jami'an jam'iyyar da ke mulkin.

Kasashen duniya dai sun sa ido domin ganin yadda zabe zai gudana a shekara ta 2018 mai kamawa a Zimbabuwe, wanda shugaba Mnangagwa ya ce za'ayi shi cikin gaskiya da adalci.