Zargin IS da PKK kan harin Turkiya | Labarai | DW | 14.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin IS da PKK kan harin Turkiya

Firaministan kasar Turkiya Ahmet Davutoglu ya ce wasu daga cikin wadanda ake zargi da kai harin da ya hallaka mutane 97 a kasar a karshen mako sun zauna a Siriya na wasu watanni.

Hare-hare sun girgiza Turkiya a karshen mako.

Hare-hare sun girgiza Turkiya a karshen Mako.

Davutoglu ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mutanen ka iya zama suna da alaka da kungiyar IS ko kuma ta tsagerun Kurdawa. Ya bayyana harin da aka kai a kan masu rajin kare Kurdawan kasar da kuma kungiyoyin fararen hula, a yayin da suke zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Kurdawan da hari mafi muni da kasar ta taba fuskanta. Ya kara da cewa harin an kai shi ne domin shafawa jam'iyyarsu da ke mulki ta AK kashin kaji gabanin zabukan da kasar za ta gudanar a ranar daya ga watan Nuwamba mai zuwa, inda ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike.