Zanga-zangar nuna adawa da taron G20 a Hamburg | Labarai | DW | 02.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar nuna adawa da taron G20 a Hamburg

Dubban jama'a a birnin Hamburg da ke a arewacin Jamus sun gudanar da wani gangami don nuna adawa da taron kasashe guda 20 masu karfin tattalin arzikin masana'antu watau G20 da za a yi a wannan makon.

'Yan sanda sun ce kamar mutane dubu goma ne suka yi zanga-zangar cikin ruwan sanhi a gaban ofishin magajin gari na birnin na Hamburg inda za a yi taron. Daya daga cikin masu gangamin ya soki lamirin kasashen na G20 da cewar su, suka fi kowa fitar da hayakin da ke gurbata muhali a duniya  amma kuma ba sa yin wani yunkuri don rage hayakin.