1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar goyon bayan matakin gwamnati kan AREVA

October 12, 2013

Al'ummar Arlit a Nijar ta fito ta yi zanga-zangar marawa matakin gwamnatin ƙasar baya, na tattaunawa da kamfanin AREVA domin tabbatar an mutunta haƙƙoƙin 'yan ƙasa

https://p.dw.com/p/19ydL
This undated photo provided by French nuclear manufacturer Areva shows workers at the uranium mine of Arlit, northern Niger. French soldiers operating out of a hotel in Niger's capital and using reconnaissance flights over the Sahara searched Monday Sept. 20, 2010 for seven foreign workers who were kidnapped near a French-operated uranium mine and seemingly swallowed by the vast desert. Armed assailants kidnapped last week seven people near the uranium mining town of Arlit, in northern Niger. Five are French, one is from Togo and one is from Madagascar. Those abducted include a man who worked for Areva and his wife, as well as five employees of a subcontractor called Satom.(AP Photo/AREVA/HO) NO SALES - MANDATORY CREDIT: AREVA
Hoto: AREVA

Dubban mutane a Nijar suka fito suka yi zanga-zangar nuna adawa da kamfanin AREVA na Faransa, wadda ke kwangilar haƙan Uranium a ƙasar na tsawon shekaru 50 yanzu.

Maƙasudin wannan zanga-zanga wadda ta sami halartar aƙalla mutane dubu biyar, shi ne goyon bayan tattaunawar da gwamnati ta shiga da kamfanin na AREVA, kamar yadda Azauwa Mamane ɗaya daga cikin jagororin gangamin ya shaida wa kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP.

Ranar lahadin da ta gabata, Firaministan ƙasar Birji Rafini ya sha alwashin cewa gwamnati zata yi bitar yarjejeniyarta da kamfanin bisa zargin cewa akwai rashin daidaito a ƙawancen da suka ƙulla,

Rafini ya kuma ce hatta kwangilolin da kamfanin na AREVA ke yi da wasu ƙananan kamfanoni ma za a yi bitan su.

Masu zanga-zanga waɗanda suka haɗa da zaɓaɓɓun wakilai na majalisa da mazauna yankin sun yi maci a titunan birnin Arlit suna raira ƙasidun dake nuna adawarsu da AREVA

Mai magana da yawun masu zanga-zangar ya ce a yanzu haka akwai kusan tonne milliyan 50 na dagwalon da masana'antar AREVA ɗin ta bari, kuma kamfanin na samar ma kanta kusan cubic meta milliyan 20 na tsabtataccen ruwa, a yayin da mutane ke fama da ƙarancin ruwa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh