1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin adawa da Yahudawa a Berlin

Yusuf Bala Nayaya
June 1, 2019

Wannan gangami da ya samu sa ido na 'yan sanda kimanin 500, na zuwa ne yayin da ake fargaba ta karuwar nuna kyama ga Yahudawan a Jamus inda ake samun labarai na afka musu.

https://p.dw.com/p/3Jbld
Berlin - Gegendemonstration zur anti-israelischen Al-Kuds-Demonstration
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Riedl

Kimanin mutane 1,200 ne suka fita zanga-zangar adawa da Yahudawa a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus a wannan Asabar sai dai irin wannan adadi kuma sun fita don nuna adawarsu ga masu nuna kyamar ga Yahudawan.

Wannan gangami da ya samu sa ido na 'yan sanda kimanin 500, na zuwa ne yayin da ake fargaba ta karuwar nuna kyama ga Yahudawan a Jamus inda ake samun labarai na afka masu.

An dai rika jin wake-wake na kin Yahudawan a bangare guda, yayin da masu goyon bayan Yahudawan ciki har da 'yan siyasa suka rika mayar da martani 'yan sanda kuwa na tsakiya don kada a kafsa fada.