Zaben ´yan majalisar dokokin Netherlands a yau laraba | Labarai | DW | 22.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben ´yan majalisar dokokin Netherlands a yau laraba

A yau laraba ake gudanar da sabon zaben ´yan majalisar dokokin kasar NL. Jam´iyun siyasa 14 na kasar baki daya suka tsayar da ´yan takarar neman shiga majalisar mai kujeru 150. An yi hasashen cewa jam´iyar FM mai ci Jan Peter Balkenende zata lashe zaben na yau. Manazarta harkokin siyasar kasar sun ce saboda bunkasar tattalin arziki da ake samu a kasar ta NL, jam´iyar ´yan Christian democrat zata yi nasara akan jam´iyar ´yan social democrat karkashin Wouter Bos. To amma ba´a tsammanin zata samu wani rinjaye na a zo a gani.