1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Zaben Turkiyya:Yan adawa ne a kan gaba a Istanbul da Ankara

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 31, 2024

Ya zuwa yanzu an kirga kashi 20 cikin 100 na kuri'un da aka kada, kuma magajin garin Istanbul na da kashi 49.6 cikin 100, yayin da 'dan takarar jam'iyyar shugaba Recep Tayyip Erdogan ke da kashi 41.6 cikin 100

https://p.dw.com/p/4eIad
Hoto: Mehmet Siddik Kaya/Anadolu Agency/picture alliance

Sakamakon farko na zaben Turkiyya na kananan hukumomi da magadan gari da kuma kansiloli da ke fitowa, ya nuna cewa 'yan adawa ne ke kan gaba, a biranen Istanbul da Ankara.

Karin bayani:Zaben kananan hukumomi a Turkiyya

Gidan talabijin din kasar ya ce ya zuwa yanzu an kirga kashi 20 cikin 100 na kuri'un da aka kada, kuma magajin garin Istanbul na da kashi 49.6 cikin 100, yayin da 'dan takarar jam'iyyar shugaba Recep Tayyip Erdogan ke da kashi 41.6 cikin 100 na kuri'un.

Karin bayani:Tarayyar Turai ta tura taimako Turkiyya

Haka zalika a birnin Ankara bayan kirga kashi 12 cikin 100 na kuri'in, magajin garin ya samu kashi 56.3 cikin 100, yayin da 'dan takarar jam'iyyar shugaba Recep Tayyip Erdogan ke da kashi 36.3 cikin 100.