Birnin Istanbul shi ne birni mafi girma a kasar Turkiyya. Birnin wanda ke arewa maso yammacin kasar na da dimbin tarihi.
Galibin harkokin kasuwanci da ake gudanarwa a Turkiyya sun fi karfi ne a Istanbul, wannan ne ma ya sanya ake kallonsa a matsayin cibiyar kasuwancin kasar. Safarar jiragen sama na kasar ta fi karfi a birnin wanda hakan ya sanya ya yi fice.