1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurkiyya

Za a zabi sabbin magadan gari a Turkiyya

Abdourahamane Hassane
March 29, 2024

A ranar Lahadi Al'ummar Turkiyya za ta kada kuri'a domin zaben magadan gari,da kansiloli. Kimani muane miliyan sittin ne za su halarci runfunan zaben domin zaben magadan gari da kansiloli sama da guda dubu.

https://p.dw.com/p/4eGJs
Hoto: Felat Bozarslan/DW

 A cewar wani hasashe na jin  ra'ayin jama'a, biranen Istanbul da Ankara za su ci gaba da kasancewa a hannun jam'iyyar 'yan adawa ta CHP,  ta Social-Democrat. An yi hasashen cewar  jam'iyya mai mulki ta AKP za ta samu koma baya a garuruwa da dama. Erdogan wanda ke kan karagar mulkin tun shekara ta  2003 ya bayyana a farkon watan Maris cewa, wadannan zabukan kananan hukumomi za su kasance zabukan karshe da aka shirya  a karkashin ikonsa,