Zaben shugaban kasa a Faransa | Siyasa | DW | 05.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben shugaban kasa a Faransa

A ranar Lahadi mai zuwa za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Faransa, inda 'yan kasar za su dauki mataki tsakanin matashi mai sassauci ko kuma 'yar ra'ayin rikau.

Frankreich Wahlplakate Macron und Le Pen 2. Runde (picture-alliance/Maxppp/L. Vadam)

'Yan takarar neman shugabancin kasar Faransa a zagaye na biyu.

'Yan kasar ta Faransa kimanin miliyan 48 za su yanke hukunci na ko dai su zabi mai ra'ayin sassauci Emmanuel Macron dan shekaru 39 ko kuma 'yar ra'ayin rikau Marine Le Pen mai shekaru 49. Ko da yake Macron ke kan gaba a kuri'ar jin ra'ayin jama'a amma ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare. Zaben dai na da muhimmanci kan rawar kasar ta Faransa cikin kungiyar Tarayyar Turai ta EU. Tuni dai wasu jaridun kasar Faransar suka yi kira ga masu zabe da su fita kwansu da kwarkwata domin kada kuri'a a ranar Lahadi da nufin hana Marine Le Pen mai ra'ayin rikau samun nasara, suna masu cewa dole kowa ya san zaben ya na matsayin kare tsarin demokradiyya ne. Fafatawar da za a yi tsakanin Macron mai sassaucin ra'ayin gurguzu daLe Pen 'yar jam'iyyar masu tsananin kishin kasa ta National Front na da muhimmanci ba ma ga kasar ta Faransa kadai ba, har ma da makwabtanta na nahiyar Turai.

Matsayin 'yan takarar Faransa kan Tarayyar Turai

Frankreich En Marche: Rund 260.000 Mitglieder innerhalb eines Jahres ( En Marche Gironde)

Masu yakin neman zabe a Faransa.

A yayin da Marine Le Pen ke adawa da manufofin kungiyar EU tana mai cewa za ta fi ba wa muradun kasar Faransa fifiko, shi kuwa a nasa bangaren Emmanuel Macron yana goyon bayan yin kwaskwarima ga tsarin tattalin arziki da zamantakewa kana dan rajin hadin kan Turai ne. A saboda haka ne ma Frank Baasner na cibiyar nazarin manufofin Jamus da Faransa da ke birnin Ludwigshafen na nan Jamus ya ce za a shiga sabon babi na dangantaka tsakanin EU da Farsansa idan Macron ya lashe zaben. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya-bayan nan dai ta nunar da cewa Macron dan shekaru 39 yana gaba da yawan kuri'u a kan Le Pen mai shekaru 49. Sai dai masana lamuran siyasa sun yi kira da a yi taka tsan-tsan domin kawo yanzu da yawa daga cikin al'ummar kasar ta Faransa ba su yanke hukunci ba na wanda za su kada kuri'arsu gare shi tsakanin Macron da Le Pen. 

Sauti da bidiyo akan labarin