1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayar AU da EU kan zaben Kwango

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 23, 2019

Kungiyar Tarayyar Turai da ta Tarayyar Afirka sun nunar da cewa za su yi aiki tare da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, biyo bayan zaben Felix Tshisekedi a matsayin shugaban kasa, a zaben kasar da ke cike da rudani.

https://p.dw.com/p/3C0Af
Belgien Treffen Außenminister AU und EU in Brüssel
Taron kungiyoyin EU da AUHoto: DW/T. Schauenberg

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan kammala taron da suka gudanar a birnin Brussels na kasar Beljiyam, koda yake ba su mika sakon taya murnarsu ga Tshisekedi wanda kotun tsarin mulki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon ta tabbatar da zabensa a karshen mako ba. Matakin nasu dai ya saba da sakon taya murna da wasu shugabannin kasashen Afirka suka aike ma da Tshisekedin jim kadan bayan da kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben. Tshisekedi da ke zaman dan takara daga jam'iyyar adawa, ya samu nasarar lashe zaben ne da kuri'un da ba su taka kara sun karya ba a gaban dan takara daga watajam'iyyar adawar Martin Fayulu a zaben da aka gudanar a Jamhuriyar Dimukuradiyar Kwangon a ranar 30 ga watan Disambar bara. Sai dai har kawo yanzu Fayulu na kan bakarsa na cewa shi ne ya lashe sama da kaso 60 cikin 100 na kuri'un da aka kada, kamar yadda a makon da ya gabata kungiyar Tarayyar Afirka AU ta nuna shakku kan sakamakon zaben.