1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben fidda gwani da zanga-zanga a Zamfara

October 3, 2018

Zaben dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Zamfara ya gagara kammala a wasu wuraren yayin da wasu wuraren kuma sam-sam ba'ayi ba sai zuwa Alhamis musamman cikin garin Gusau inda aka fuskanci matsaloli.

https://p.dw.com/p/35vvF
Nigeria Vorwahl im Bundesstaat Zamfara
Hoto: DW/Y.I. Jargaba

Tun karfe shida na safe dai kusan dukkanin al'ummar kananan hukumomin 14 da ke jihar ta Zamfara Arewa maso Yammacin Najeriya suka yi fitar kwarin dango don jefa kur'arsu sai kuma abun ya sha bam bam har ta kai ga haifar da zanga-zanga wadda ta kai ga  fasa gilasan motocin masu bin babbar hanyar zuwa Sokoto ta karamar hukumar Bungudu.

Wannan zanga-zanga dai ta kunshi maza da mata inda kowa ke fadin albarkacin bakinsa wasu na korafi na cewa an ki cika masu alkawura da aka yi a baya.

Ko me ya haifar da jan kafa wajen raba kayan zaben kamar yadda akai wa al'umma alkawari Yusuf Dan Umma mamba ne na kwamitin da uwar jam'iyyar ta kasa APC ta aike jihar Zamfara dan gudanar da zabe: "Yadda muka tsara don tabbatar da zaben ya yi kyau tin jiya muka raba kayan zabe mun kuma tabbatar mun zabi amintattun mutane wadanda za su gudanar da zaben nan, sannan tunTalata mun sa kayan zaben a ofishin 'yan sandan kananan hukumomin jihar kawai Laraba da safe sai muke samun rahotan karanci takardun kada kuri'a."

Za dai a kammala zabuka a wuraren da ba a yi ba a ranar Alhamis idan Allah ya kaimu.