Za mu kawo karshen ta′addanci a Najeriya-Jonathan | Labarai | DW | 08.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za mu kawo karshen ta'addanci a Najeriya-Jonathan

Shugaban Najeriya ya sha alwashin ceto dalibai 'yan matan nan da aka sace daga wata makarantar sakandare da ke Chibok jihar Borno.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sha alwashin gano dalibai 'yan mata fiye da 200 da 'yan tawayen Muslmi suka sace, yana mai cewa ceto su zai bude wani babi na kawo karshen ayyukan ta'adanci a kasar. A lokacin da yake jawabi a taron tattalin arzikin duniya kan Afirka da ke gudana a birnin Abuja, Jonathan ya gode wa kasashen ketare ga taimakon da suke bayarwa a kokarin ceto 'yan matan wadanda aka yi garkuwa da su daga wata makarantar sakandare da ke Chibok a ranar 14 ga watan Afrilun da ya gabata. Ya kuma mika godiya ga mahalarta taron da ya ce sun hallara duk da barazanar da ake fuskanta daga masu ta da kayar baya. Shugaban ya kuma yi magana game da kirkiro aikin yi a kasashen Afirka.

A kan haka hanshakin dan kasuwar nan na Najeriya Aliko Dangote ya ce zai zuba jari na kimanin dalar Amirka miliyan dubu 2.3 a bangaren samar da sukari da noman shinkafa a arewacin Najeriya. Dangote da ke zama mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka ya fada wa taron tattalin arzikin duniya a Abuja cewa kirkiro da aikin yi shi ne muhimmin makamin magance matsalar rashin tsaro a yankin. Ya kuma ce zai zuba jarin dala miliyan dubu 12 a Najeriya da kuma dala miliyan dubu hudu a wajen kasar a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Mawallafi: Mohamad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu