Za mu ci gaba da hulda da Amirka - Ramaphosa | Labarai | DW | 17.09.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za mu ci gaba da hulda da Amirka - Ramaphosa

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce kasarsa ta amince ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da Amirka kan lamuran da suka danganci kiwon lafiya da tsaro da kuma alkinta muhalli.

Ramaphosa ya ambata hakan ne a jiya Juma'a, a lokacin da ya ziyarci takwaransa na Amirka Joe Biden a Fadarsa ta White House, inda ya bukaci Amirka din da ta kaucewa daukar duk wani kakkausan mataki kan kasashen Afirka  ke ci gaba da yin hulda da gwmanatin Shugaba Vladmir Putin na kasar Rasha.

Shugaban na Afirka ta Kudu ya ce duk wani mataki da za a dauka kan kasashen da ke da alaka ta kut da kut da Rasha zai taimaka wajen yin illa ga wannan kasa da kuma mayar da ita saniyar ware wanda hakan zai shafi cigabata matuka.

Wannan kira na Ramaphosa na zuwa ne bayan da majalisar dokokin Akirka ta amince da wani kuduri da aka gabatar mata kan daukar matakai na dakile irin karfin dangantakar da ke akwai tsakanin Rasha da wasu kasashen Afirka.