Za a yi taro kan Siriya a Astana | Labarai | DW | 17.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a yi taro kan Siriya a Astana

Taron zai hada kasashen Iran da Turkiya da kuma Rasha domin tattauna batun yakin Siriya.

Babban jami'n diflomasiya na kasar Rasha Serguei Lavrov ya ce daya daga cikin manufofin da ake da su a taron da kasashen Rasha da Turkiya da Iran za su yi a ranar 23 ga wannan wata  a Astana shi ne na kara tabbatar da shirin tsagaita wuta a Siriya.Kasashen Rashar da Iran na goyon bayan gwamnatin shugaba Bashar Al Assad yayin da Turkiyar ke goyon bayan 'yan tawayen Siriyar.