1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunci kan wanda ya yi wa yarinya fyade kafin kisa

Ramatu Garba Baba
July 10, 2019

Wata kotu a Jamus za ta yanke hukunci kan wani dan asalin kasar Iraki da ake tuhuma da laifin kisan wata yarinya mai shekaru 14 bayan da ya yi mata fyade.

https://p.dw.com/p/3LqHr
Wiesbaden Prozessauftakt im Fall Susanna Anwalt
Hoto: Getty Images/AFP/B. Roessler

Ali Bashar dan shekaru ashirin da biyu da haihuwa, ya na daga cikin 'yan gudun hijirar da Jamus ta ki amincewa da bukatarsu ta neman mafaka. An dai karfafa tsaro a harabar kotun a gabanin hukuncin na wannan Laraba. Ali zai fuskanci hukunci na daurin rai da rai muddun kotu ta tabbatar da laifukan biyu da ake tuhumarsa a kai.

Masu shigar da kara sun bayar da labarin yadda bayan gallazawa yarinyar azaba kafin fyade da kisan, daga bisani ya bar gawar a cikin daji. Ali tare da sauran danganinsa sun tsere daga Jamus zuwa Iraki, amma da taimakon 'yan sandan kasa da kasa aka cafke shi aka kuma dawo da shi don fuskantar hukunci.

Kisan Susanna Maria Feldman, yar shekaru goma sha hudu a watan Mayun da ya gabata , ya haifar da muhawara inda Jam'iyyar masu tsatsauran ra'ayi ta AfD ta yi amfani da batun don nuna adawarta da shirin Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel na son bai wa dubban baki mafaka.