Za a tattauna batun Gambiya a Ghana | Labarai | DW | 06.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a tattauna batun Gambiya a Ghana

Shugabannin da za su je bikin rantsar da sabon shugaban kasar na Ghana dabra da taron za su tattauna rikicin siyasar Gambiya.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya mai shiga tsakanin a rikicin siyasa na Gambiya,inda shugaba Yahya jammeh ya fadi a zaben shugaban kasa ya yi mursisi ya ki sauka.Ya ce a gobe Asabar a wajen taron rantsar da sabon shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo a  birnin Accra shugabannin kasashen na Afirka za su tattauna batun na Gambiya tare da samar da hanyoyin samun mafita a rikicin.Kakakin shugaban Najeriyar Garba Shehu wanda ya sanar da wannan labari ya ce Muhammadu Buhari ya sha alwashin warware matsalar siyasar ta Gambiya.