Za a Karfafa ayyukan agaji a tafkin Chadi | Labarai | DW | 21.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a Karfafa ayyukan agaji a tafkin Chadi

Kungiyar bada agajin gaggawa ta CICR ta sanar da aniyarta ta fadada ayyukanta a kewayen tafkin Chadi, inda rikici ya sa dubunnan mutane barin matsugunnansu.

Peter Maurer

Peter Maurer

Yayin da yake magana kan wannan batu, Shugaban Kungiyar ta CICR Peter Maurer, ya ce za su fadada ayyukan kungiyar Red Cross a kasashen Kamaru, Chadi, Nijar da kuma Najeriya, inda ya ce mutanen garuruwa gaba daya sun bar gidajansu cikin matsananciyar wahala sakamakon matsalar Boko Haram.

Shugaban wannan kungiya ya kara da cewa, ko da fadace-fadacen za su kawo karshe a gobe, to fa za'a shafe tsawon shekaru ana ayyuka a wannan yanki kafin mutanen su samu dawowa cikin hayyacinsu.

Yawan kudadan da za'a yi amfani da su wajan agajin gaggawar a kewayen na tafkin Chadi, ya kai a kalla Euro milian 106, abun da ke nunin cewa, matsalar 'yan gudun hijirar a kewayen na tafkin Chadi, itace ta uku a fadin duniya, bayan ta kasar Siriya da kuma Sudan ta Kudu.