Za a kara agaji a Ghouta | Labarai | DW | 08.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a kara agaji a Ghouta

Rahotannin daga Syria na cewa tawaga ta biyu ta kayan agaji zata isa gabashin Ghouta a wannan Alhamis, makonni uku bayan fuskantar tsananin hare-hare daga dakarun kasar da jiragen yakin Rasha.

Syrisch-Arabischer Roter Halbmond Hilfsorganisation (Getty Images/L. Beshara)

Motoci dauke da kayan agaji

Hare-haren na kasashen biyu sun janyo martani daga kasashen duniya, baya ga amincewar da Majalisar Dinkin Duniya na a tsagaita budawa juna wuta, abin ma da ya kai MDD ga bayyana hakan a matsayin mataki ne na neman ruguza gabashin na Ghouta baki daya.

Alkaluma dai sun yi nunin cewa sama da mutum 860 ne suka mutu, wasu da dama kuwa na fama da raunuka tun bayan kaddamar da wuta da gwamnati shugaba Assad ta yi a ranar 18 ga watan jiya. Gabashin na Ghouta da ke wajen birnin Damascus, waje ne da gwamnatin ta Syria ke cewa da ya saura a hannun mayakan tawaye.