Yunkurin tabbatar da tsaro a wasu kasashen Sahel | Siyasa | DW | 21.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunkurin tabbatar da tsaro a wasu kasashen Sahel

Kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso na kokarin yin amfani da tsarin bai daya na ba da 'yanci gashin kai ga yankunan kasashen a wani mataki na kara daukar matakan tsaro domin yaki da ta'addanci.

Shugabannin kananan hukumomin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar mambobi a kungiyar raya kasashen ta Liptako Gourma na ci gaba da zaman taro kan zaman lafiya da matakin cimma burin kafa tsarin bai wa kananan hukumomi ragamar cin gashin kai. Ana kokarin kaddamar da wannan shiri ne wanda aka dade ana yi tunani a kansa tare da tallafin Jamus da hukumar raya kasashe ta MDD. Wakilai daga kasashen guda uku da ke yin taro a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar sun ce wannan mataki ne na farko kafin a kai ga cimma kafa wani kwamitin da zai kula da jagorancin wannan aiki da zai kara karfafa tsaro a cikin kasashen guda uku.

 

Sauti da bidiyo akan labarin