Yunkurin sasanta mabiya addinai a Nijar | Zamantakewa | DW | 27.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yunkurin sasanta mabiya addinai a Nijar

Wasu a Jamhuriyar da ke kungiyar CDIR wadda ke sulhunta mabiya addinai daban-daban na cigaba da fadakar da al'umma mahimmacin zaman lafiya da fahimtar juna.

Su dai wadanan matasa Pasto Sulemane Ibrahim da Ustaz Ashiru Malam Tukur matasa ne da ke zaman mambobi na kungiyar fahimtar juna tsakanin adainai ta birnin Maradi, sun kuma sadaukar da rayuwarsu wajen wayar da kan 'yan uwansu da sauran al'umma kan hanyoyin inganta kyaukyawar zamantakewa tsakanin mabiya adini Kristanci da Musulunci.

31.10.2013 DW Karten online Niger eng

Jamhuriyar Nijar ta kunshi mabiya kabilu da addinai daban-daban

Wannan aikin da matasan suka fara dai na cigaba da tasiri tare da kawo sauyi da ma cigaba a tsarin zamantakewa. Abin mamaki dai shi ne yadda wadanan matasa ke aiki da ba tare neman wani dan abin masarufi daga hannun hukumomi ko kuma masu hannu da shuni ba.

Wadannan matasa dai wato Fasto Ibrahim da Ustaz Tukur kan shirya taruka da lakcoci domin fadakar da mutane, batun da ya sanya hukumomi da sauran al'umma ta Musulmi da Kirista yin Allah san barka da wanna kokari nasu. Yanzu haka dai aikin nasu ya fara game wasu sassan Afirka ciki kuwa har da tarayyar Najeriya da nufin ganin sun taimaka wajen shimfida zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.