Yunkurin sake farfado da daukacin hanyoyin sufurin jirgin kasa a Najeriya | Siyasa | DW | 09.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunkurin sake farfado da daukacin hanyoyin sufurin jirgin kasa a Najeriya

A wani abin da ke zaman yunkurinta na sake farfado da hanyoyin sufurin jirgin kasa a tarrayar Najeriya, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon layin dogon da zai hade biranen Fatakwal da Maiduguri.

Sabon aikin shimfida layin dogon da zai lashe Dalar Amurka miliyan dubu uku na zaman rabi kudi rabi kuma bashi tsakanin tarrayar Najeriya da za ta kashe kaso 15 cikin 100 na daukacin kudin, da kuma kasar Sin da za ta ba da ragowar kaso 85 cikin 100 da ake da bukata.

Kuma ko bayan layin dogon za a  samar da wata tashar jirgin ruwa a tsibirin Bonny da ke jihar Rivers da kuma wata farfajiyar ciniki a garin na Fatakwal a wani abin da ke zaman alamun karin daraja a cikin harkar sufurin jirgin kasa a Najeriyar.

Karin bayani: Najeriya: Gwamnati na kokarin fadada harkar sufurin jiragen kasa

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya dai bai boye ba bisa ga burin 'yan mulki na sauya makomar daukacin yankunan guda biyu da ke da tasiri bisa ga tattali na arziki da zamantakewa ta kasar.

"Babban burin kasarmu na inganta ababe na more rayuwa da layin dogon ya dada girma tare da wadannan ayyuka guda uku da aka tsara su domin dogaro da juna a wajen aikinsu. Layin Fatakwal zuwa Maiduguri dai an tsara shi ne ya sake farfado da harkoki na tattalin arziki cikin yankin da ta'addanci ya mayar can baya. Haka kuma hade layin dogon da sabuwar tashar jirgin ruwa ta tsibirin Bonny da kuma wata cibiya ta kasuwancin da ake sa ran layin dogon zai inganta a Fatakwal, zai taimaka wajen habbaka ciniki a cikin yankin yammacin Afirka da kuma daukaci na kasuwa ta bai daya ta kasashen Africa."

Shugaba Buhari bayan kaddamar da layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna a 2016

Shugaba Buhari bayan kaddamar da layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna a 2016

Akalla kwantainoni dubu 500 ne dai aka tsara layin zai rika dauka a shekara daga birnin Maiduguri da kuma garuruwan da ke kusa ya zuwa cibiyar cinikin ta Fatakwal da kuma tashar jirgin ruwa ta Bonny.

Karin bayani: Bunkasa ciniki: Layin dogo tsakanin Najeriya da NijarKuma a fada ta ministan sufurin na kasa Rotimi Ameachi, ko bayan sake mai da tsohuwa yarinya, a nan gaba kuma Abujar na da niyyar sake ginin wani layin dogo na zamani mai tsawon kilomita 1500 a gabashin tarrayar Najeriyar.

"Bukatar layin dogo mai aiki na ci gaba da karuwa a yankin gabashin Tarrayar Najeriya, sakamakon raguwar hanyar sufurin kaya tsakanin sassa na kasar. Akwai raguwar samar da bukatu na rayuwa irin na su dabbobi, da ma'adinai, da karafa da man fetur da bukatu da yawa, abin kuma da ya rage ayyukan masana'antu, da kuma tsadar kayayyaki na rayuwa. Gwamnatin tarraya na son rage wannan. A matsayin ministan sufuri mun samu amincewa guda biyu, na farko shi ne sake farfado da layin dogon da ke kasa, sannan kuma daga baya mu sake gina sabo na zamani mai tsawon kilomita 1500, in mun samo bashi. A yayin kuma da muke neman wannan bashi to za mu fara mai da tsohuwa yarinyar."

Ya zuwa yanzu dai kusan daukacin layukan dogo guda biyar a kasar ko dai ta yi nisa a cikinsu, ko ta kammala, ko kuma take shirin farawa dai an ciwo su da bashi, a wani abin da ke nuna irin karkatar kasar zuwa ga basukan waje a hanyar ingantar sufurin da kasar ke yiwa kallon gada tsakaninta da komawa ta zamani.

Sauti da bidiyo akan labarin