1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin take hakkin masu bore

Ramatu Garba Baba
November 29, 2022

Shugabanin kasashen duniya sun damu da yunkurin mahukuntan Chaina na tauye 'yancin 'yan kasar da ke zanga-zangar adawa da dokar kullen corona.

https://p.dw.com/p/4KD6p
Jami'an tsaro da masu adawa da dokar kulleHoto: Thomas Peter/REUTERS

Shugaban kasar Jamus Frank Walter Steinmeier ya yi kira ga mahukuntan kasar Chaina kan su mutunta 'yancin masu zanga-zanga. Steinmeier ya bi sahun sauran shugabanin kasashen duniya da Majalisar Dinkin Duniya na yin kira ga mahukuntan na Chaina, a game da kare hakkin bil'adama a kasar da al'ummarta ke zanga-zangar adawa da matakan dokar kullen corona da ta sanya.

Wannan na zuwa ne bayan da rahotannin suka soma nuna yadda jami'an 'yan sanda ke amfani da karfi kan masu boren. Sannu a hankali zanga-zangar da aka soma daga birnin Shanghai na bazuwa zuwa sauran biranen kasar.

Duk da cewa gwamnati ta sassauta wasu daga cikin dokokin don kwantar da hankalin jama'a, amma har yanzu ba a soke dokar kullen da ta haifar da gagarumin gangamin da ya kasance babban kalubale ga shugabancin Xi Jinping da jam'iyyarsa ta kwaminansanci ba.