Yunkurin kai hare-hare a Maiduguri | Labarai | DW | 14.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin kai hare-hare a Maiduguri

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce ta dakile wani yunkuri na mayakan Boko Haram na kai wasu jerin hare-hare, ciki har da na kunar bakin wake a Maiduguri.

Chris Olukolade

Chris Olukolade

Kakakin rundunar tsaron Janar Christ Olukolade ne ya shaidawa manema labarai cewa, wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan Kungiyar Boko Haram ne da ke neman tsere wa daga dajin Sambisa suka nemi kai hare-hare a barikin sojoji na Giwa da ke Maiduguri amma kuma hakarsu bata cimma ruwa ba. Rahotanni dai sun nunar cewa tun da misalign karfe 6:20 na yammacin jiya Laraba (13.05.2015), al’ummar garin na Maiduguri suka shiga babbar damuwa ta sabili da karan harbe-harben bindigogi da fashewar ababe da ake zaton bama-bamai ne da aka dauki tsawon lokaci ana yi, lamarin da ya jefa al’umma da dama cikin tsoro. Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani na wata hasara rayuka ko kuma jikata, inda jama’a suke ci gaba da harkokin su na yau da kullun.