Yunkurin inganta makomar ′yan gudun hijira | Siyasa | DW | 03.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunkurin inganta makomar 'yan gudun hijira

Manyan jami'an kasashen yankin tafkin Chadi sun duba hanyoyin taimaka wa mutanen da hare- haren Boko Haram ya tagayyara a Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar ta hanyar kyautata makomarsu.

Sarakunan gargajiya da 'yan gudun hijira da jami'an gwamnati na daga cikin wadanda suka halarci taron na birnin Ndjamena. Babban batun da Hukumar da ke kula da raya tafkin Chadi ta sa gaba shi ne daukar matakan tsugunar da 'yan gudun hijira bayan gama yakar 'yan Boko Haram. A Takaice dai shugabannin na son masinta da 'yan kasuwa da suka kaurace wa sana'o'insu su sake gudanar da ayyukansu na yau da kullum kamar yadda suka saba.

Lucas Isaac shugaban 'yan gudun hijirar Najeriya a sansanin Minawao na Kamaru ya ce duk da cewa suna shirye-shiryen komawa gida, amma ba su san abin da ya kamata su yi ba kafin su koma. saboda haka ne suka halarci wannan taro domin a warware musu zare da abawa. Ita kuwa Falmata Sani, wata 'yar gudun hijira ta yi korafi kan rashin jari da za su dogara a kai wajen gudanar da harkokin kasuwanci idan suka koma gida Najeriya.

Kwamishinan shari'a na jihar Borno Barrista Kaka Shehu Lawal  ya ce gwamnatin jiharsu ta fara gina gidajen wadanda 'yan ta'adda suka kora saboda mutane su koma matsugunansu. Gwamnatin tarayyar najeriya da ta jihar Borno ne suka hada gwiwa wajen gudanar da aikin na gina sabbin matsugunai ga 'yan gudun hijira da ke komawa gida.

Wasu 'yan Boko Haram da suka tuba sun halarci taron, inda suka yi nadaman ayyukan da suka tagayyara al'umma da suka aikata.

Sauti da bidiyo akan labarin