Yunkurin canjin sheka daga APC zuwa PDM | Siyasa | DW | 19.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunkurin canjin sheka daga APC zuwa PDM

Wani bangare na 'ya'yan tsohuwar jam'iyyar CPC da suka hade cikin APC sun yi yunkurin shiga sabuwar jam'iyyar adawa ta PDM. Lamarin da ke da illa ga alkiblar da aka dosa.

Bangaren magoya bayan Sanata Rufai Hanga da ba su boye rashin jin dadainsu game da yadda aka yi masu a CPC ba, su ne ke yunkuri shiga sabuwar jami'yar ta PDM. Lamarin da ya zo wa sabuwar gamayyar Jam'iyun adawa ta APC a bazata. Tuni ma masharhanta ke bayyana shi da abin da zai iya yi wa gwagwarmayar adawa na karbe madafun iko mummunar barna.

A lokacin da DW ta tambayi Sanata Rufai Hanga abin da ya yi zafi alhali sun bayyana cikakken goyon bayansu ga APC? Cewa ya yi"Tun farko CPC din nan da aka taso, ana ta cewa ba za'a yi da su wane ba, kuma da aka zo hadewar mutane da daman a jam'iyar CPC nan a jihohin Najeriya an ki yarda ma a yi da su,duk da goyon bayan da suke bayarwa."

Rauni ga yunkurin kayar da bangaren da ke mulki

An fuskanci rarrabuwar kawuna a APC tun ma kafin a kai ga zaben shugabanin da zasu ja rabamar jamaiyyar. Saboda haka ne ake nuna damuwa a kan illar da wanan ka iya yi ga yunkurin da aka dade ana yi na samun hadin kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyar adawar ta APC. Ko wacce illa wannan lamari ka iya yi wa jam'iyar a yanzu? Dr Usman Mohammed masanin kimiyyar siyasa da ke Abuja. Ya ce " iIla ita ce jam'iyun da suka yi wannan hadaka za su zo su yi nadaman hadewa wuri guda da suka yi idan ba'a yi hankali ba. Don haka tun yanzu ya kamata a yi wa tufka hanci."

Duk da wannan damuwa ta fuskantar rarrabuwar kawuna a jami'yun adawar Najeriya, Sanata Rufai Hanga da ke tsakiyar wannan al'amari ya ce akwai bukatar a fahimci halin da ake ciki a yanzu. Baraka ko makarkashiyar rage wa jam'iyar ta APC karfi dai batu ne da aka dade ana hasashe da ma sauraren faruwarsa, domin kuwa tun bayan yi wa jam'iyar rejista ta shiga yakin cacar baka da jam'iyar PDP da ke mulkin Najeriya.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mouhamadou Awal

Sauti da bidiyo akan labarin