1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkuri sasanta rikicin APC a Najeriya

February 7, 2018

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya fara shirin sulhunta tsakanin 'ya'yan jam’iyyar da nufin hada kai kafin tunkarar gwagwarmayar zaben 2019.

https://p.dw.com/p/2sFRc
Lagos Taslim Balogun - Bola Tinubu
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi

A wasu jihohi dai an kai har ga zagi-in-zaga a yayin kuma da wasu aka kai har ga nunin yatsa kuma duk a tsakanin 'ya'yan jami'iyyar APC mai mulki da suka yi nisa a cikin rabuwa sannan kuma ke shirin fuskantar zaben a gaba.

Kama daga jihar kano ya zuwa ta Zamfara dama 'yar tsakiya ta Kaduna dai ta yi baki  tana kuma nuna alamun lalacewa a tsakanin 'ya'yan APC da ke a rabe  a bisa makomar zaben da kuma yanzu haka Abujar ta ce tana bukatar gyarawa.

Tuni dai fadar gwamnatin kasar ta mika alhakin sassanta tsakanin a bisa tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu da ta ce ya zabi 'yan kwamitin da yake so domin daidaita  tsakanin  'yan APC da ke bukatar  hawa sahu a fadar Mallam  Garba Shehu da ke zaman kakakin fadar.

Nasarar sake kulle masu tsintsiye ko kuma kokari na fara zub da yawun hauka dai, rigingimun na daukar fasali iri daban daban  a matakai na jihohi daban daban.

Can a jihar zamfara inda ake takun saka a tsakanin gwamnan jihar Abdul'azeez Yari da kuma dan majalisan dattawan da ke wakiltar al'ummar jihar Senata Kabiru Marafa dai game da misali, batun tsaron cikin jihar dai na zaman ummul'aba'isin tada hankalin bayan zargi gwamnan da hannu da kafa a cikin rikicin.

Nigeria Präsident Muhamadu Buhari
Buhari da wasu jami'an APCHoto: Novo Isioro

 

Zargin juna da goyon bayan masu mulki

Zargin kuma da magoya bayan gwamnan ke yi wa kallo yana kama da siyasa ga Marafan dan jam'iyya mai mulki kuma sabon jagora ga adawa a fadar Sani Gwamna Mayanci da ke zaman daya a cikin masu goya bayan gwamnan.

Irin wannan jerin rigingimun ne dai ya kai ga tsohuwar jam'iyyar PDP mai mulki samun matsala, sakamakon jerin rigingimun cikin gida sannan kuma da nuna fifikon mahukuntan na Abuja.

Shi kansa sabon rikicin dai a tunanin Dr Umar Ardo da ke sharhi a bisa harkoki na siyasar Tarrayar Najeriyar dai na zaman alamun rushewar jam'iyyar da shugaban kasar ya kwacewa aiki yanzu.

Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin wadanda Buharin ke kokari na neman sulhuntawar da kuma masu tunanin yana bukatar sake ginin jam'iyyar gaba daya.