Yemen: Pakistan za ta taimakawa Saudiyya | Labarai | DW | 30.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yemen: Pakistan za ta taimakawa Saudiyya

Pakistan ta ce za ta tallafawa Saudi Arabia da sauran kasashen yankin Gulf da ke yakar 'yan tawayen kungiyar Houthi mabiya tafarkin shi'a da ke son karbe iko da Yemen.

Ministan harkokin wajen Pakistan din Khawaj Asif ya ce wata tawagar gwamnati daga kasar wadda zai jagoranta za ta je Saudi din a Talatar nan don tattaunawa kan wannan batu.

Gabannin wannan zantawa da kasashen biyu za su yi, ministan tsaron Pakistan din da shugabannin rundunonin tsaro na kasar gami da firaminista Nawaz Sharif sun yi wata ganawa kan tallafawa Saudi din a yakin da ta ke da 'yan tawayen Yemen. Pakisan dai na daga cikin kasashen da ke dasawa da Saudi Arabiya.