1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara miliyan 72 na aikatau a Afirka

Abdul-raheem Hassan
June 12, 2021

Karuwar adadin yara da ke cikin aikin karfi babbar barazana ce, na tabbatar da muradun cigaba masu dorewa na Majalisar Dinkin Duniya na kawar da aikatau tsakanin yara nan da shekarar 2025.

https://p.dw.com/p/3unRm
TABLEAU | Internationaler Tag gegen Kinderarbeit 2021 | Malawi, Lilongwe
Hoto: Amos Gumulira/AFP/Getty Images

Ministan raya cigaba na kasar Jamus Gerd Müller, ya nuna damuwa kan yawaitar yara miliyan 160 da ke aikatau a ma'aikatun sarrafa abinci da kamfanonin mulmula karafa a yammacin duniya.

Kungiyar kwadago ta duniya ILO, ta ce matsalar sa yara aikatau ya fi muni a kasashen Afirka da kusan yara miliyan 72, inda cikin kowane yara biyar ana samun akalla yaro daya dake aiki.

Ayyukan noma na daukar kashi 70 cikin 100 na ayyukan da kananan yara suka fi yi a duniya, sai ayyukan yau da kullum da kaso 20, sannan ayyukan masana'antu da kashi 10. Sai dai aikatau na yara ya fi yawa a karkara da kashi 14 cikin dari, adadin da ya ninka har sau uku a birane.

Yaki da aikatau tsakanin yara na bukatar matakin gaggawa daga kowane bangare, duk da cewa an danganta annobar corona da taka rawar maida hannun agogo baya.