Yawan wadanda suka rasa rayukansu a hadarinjirgin Najeriya ya karu | Labarai | DW | 12.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yawan wadanda suka rasa rayukansu a hadarinjirgin Najeriya ya karu

A Najeriya, yawan mutane da suka rasa rayukansu a cikin hadarin jirgin sama a birnin Port Harcourt, ya karu, yayinda mutane 4 daga cikin 7 da suka tsira da ransu cikin hadarin jirgin Saman suka rasu a asibiti, sakamakon raunuka da suka ji a lokacin hadarin.

Jirgin na kanfanin Solsoliso ya taso ne daga Abuja zuwa birnin PortHarcourt yayinda ya kama wuta a lokacinda ya sauka.

Wannan shine hadarin jirgin sama na biyu a Najeriya cikin watanni 2 wadda yayi sanadiyar rayukan mutane da dama.