Karuwar hare-haren Boko Haram a Najeriya
November 22, 2018Dangane da yadda ake samun yawaitar kai hare-haren ta'addanci daga kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ministan tsaron Najeriya ya doshi kasashen Chadi da Kamaru da nufin tattaunawa kan batun biyo bayan hallaka sojojin Najeriya masu yawan gaske a cikin wannan makon da ake zaton yawansu ya kai kimanin 44, a harin da kungiyar ta kai a wasu kauyuka masu iyaka da jamhuriyar Nijar.
'Ya'yan kungiyar ta ta'adda dai sun share kwanaki dai dai har guda uku, suna hari a sansanin sojojin tarrayar Najeriyar guda uku a kauyen Matele a farkon mako. Yanayin da ya janyo tada hankali har a Abuja inda ministan tsaron na tarayyar Najeriya janar Mansur Dan Ali ya yi wata ganawar sirri da shugaban kasar a kan batun.
Janar dan Alin dai ya ta'allaka sabbabin hare-haren a kan sojin kasar da janyewar sojojin Chadi da ke bada kariya ga sojin tarrayar Najeriyar daga baya. ko bayan matsalar janyewar Chadin, ana kuma kallon share tsawon lokaci wuri guda a bangare na sojin tarrayar Najeriyar na haifar da karin gajiya a bangare na sojojin da wasunsu sun share shekaru suna filin dagar mai hatsari. A dai bayaninsa, ministan ya ce suna kokarin tunkarar matsalar da gaggawa.
A baya dai manyan hafsoshin sojin kasar, sun dauki lokaci suna ikirarin cin dunduniyar kungiyar, kafin sababbabin hare-haren da ke nuna jan aikin da ke gaban mai gona, a kokari na kai biri gidan tarihi.Ko da yake ministan ya ce sabbabin hare-haren ba alama bace ta fin karfin sojin, daga bangaren Boko Haramun din da ke dada nuna karfinsu.
Sabbabin hare-haren da ke zuwa a dai dai kadowar siyasar kasar dai, na zamewa sabuwar barazana ga tarrayar Najeriyar da ke fatan zabe a ko'ina a cikin hali na lafiya, amma kuma ke kallon wannan annoba ce da ke neman kunno kai.