Yau DW ke kaddamar da talabijin da Turanci | Labarai | DW | 22.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yau DW ke kaddamar da talabijin da Turanci

Daga Litinin 22 ga watan Yuni na 2015 tashar talbijin ta DW ke fara watsa shirye-shiyenta na Ingilishi, tare da bayar da labarai sa'o'i 24 ba kakautawa a kowace rana.

Tashar ta DW ta yi tanadin wakillai a yankuna daban-daban na duniya don cimma wannan manufa. Kuma hakan na zuwa ne yayin da wannan rana ce kuma ake bude babban zaman taron shekara-shekara da tashar ta DW ke shirya wa a nan Bonn na "Global Media Forum" inda ake gayyatar da mutane daga bangarorin daban-daban na duniya. Da yake magana kan wannan batun, Darekta Janar da DW Peter Limbourg ya ce:

" Duk duniya ta sanmu da fadin gaskiya, da kuma ingancin aiki ba tare da goyon wannan ko wancan bsngare ba a fannin bayar da labaranmu. To wannan mataki namu ne muke son karfafawa a yau. Kuma muna tsammani kasar Jamus na kara daukan hankullan al'ummar duniya don haka, tare da wannan sabon tsarin da muka kawo, zamu iya samar da bayannai masu kayatarwa tare da ra'ayoyin kasar Jamus a cikin labaran duniya. Domin muna son baiwa masu kallonmu bazata...."