1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar girka gwamnatin ƙawance a Jamus

October 21, 2013

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na ƙokarin warware ƙalubalen da zai bata damar kammala girka gwamnatin ƙawance da take buƙata wajen aiwatar ayyukanta

https://p.dw.com/p/1A3ef
Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) und Bayerns Ministerpräsident Horst Seehofer (CSU) kommen am 17.10.2013 in Berlin mit (l-r) Bundesinnenminister Hans-Peter Friedrich (CSU), dem Chef des Kanzleramtes, Ronald Pofalla (CDU), dem Vorsitzenden der CDU/CSU-Bundestagsfraktion, Volker Kauder, dem Ministerpräsidenten von Sachsen, Stanislaw Tillich (CDU), dem bayerischen Ministerpräsidenten Horst Seehofer (CSU), dem Ministerpräsidenten von Hessen, Volker Bouffier (CDU), und Bundesverkehrsminister Peter Ramsauer (CSU) zur dritten Runde der Sondierungsgespräche zwischen CDU/CSU und der SPD. Foto: Wolfgang Kumm/dpa
Hoto: picture-alliance/dpa

Ranar talata ce majalisar dokokin Bundestag zata zauna a karon farko tun bayan zaɓen da jam'iyya mai mulki ta CDU ta lashe, amma kuma ta gaza samun rinjaye a majalisar, lamarin da ya sanya ta neman abokiyar ƙawancen girka gwamnati kamar yadda dokokin ƙasa suka tanada. Wannan zamar ta kasance mai mahimmancin gaske domin ita ce zata share fagen irin haɗakar da za a ƙulla, wanda kuma zai samar da irin manufofin da zasu jagoranci aƙallar sabuwar gwamnatin.

Jagororin jami'yyar SPD sun amince su shiga tattaunawa da jami'yya mai mulki wato CDU ta Angela Merkel, Jamiyyar ta yanke wannan shawarar ce bayan manyan wakilanta 200 suka yi alkawarin cimma matsaya a wasu daga cikin manufofin da jami'yyarsu take fafutukan ganin an aiwatar, waɗanda suka haɗa da ƙari a yawan mafi ƙarancin albashi da ma waɗansu buƙatu goma da suka ce ba zasu lamunta ba

Yunƙurin gudanar da tattaunawa

Ɓangarorin zasu ƙaddamar da tattaunawa kan waɗannan manufofi da ma yadda za a raba muƙamai ne ranar laraba mai zuwa, kuma ana kyautata zaton zai ɗauki wata guda ko fiye.

Jamiyyar CDU ta Angela Merkel ta yi imani ne da samar da kasafin kuɗi irin wanda bai wuce gona da iri ba, da kuma tsuke bakin aljihun gwamnati kamar yadda take ƙoƙarin gayawa takwarorinta na Tarayyar Turai, yanzu babban ƙalubalen da ke gabanta shi ne ta sassauta wasu daga cikin waɗannan manufofin na ta, ta rungumi na jamiyyar SPD waɗanda ke neman faɗaɗa kasafin kuɗin manyan garuruwa da biranen Jamus

A cewar shugaban jami'yyar ta SPD Sigmar Gabriel, wannan sabon matsayi ne za a sanya, wanda zai kasance misali ga sauran jami'yyu domin mambobin jamiyyar tasa waɗanda suka kai kusan dubu 470 zasu fara da kaɗa ƙuri'ar ko sun amince a shiga wannan haɗaka kuma har an riga an sanya ranar gudanar da babban taron jamiyya a tsakiyar watan Nuwamba mai zuwa

Sigmar Gabriel beim Pressestatement zum außerordentlichen SPD Parteikonvent im Willy-Brandt-Haus. Berlin, 27.09.2013
Sigmar Gabriel shugaban jami'yyar SPDHoto: picture alliance/Geisler-Fotopress

Rawar jami'yyar adawa na SPD

"A gani na, wannan abun koyi ne muka samar, domin muna so mu nuna cewa duk wani mamba a jam'iyya, a wannan karon, jami'yyar SPD yana da ikon faɗa a ji idan har akwai wani batun dake tattare da sarƙaƙiya. Zamanin da mutane ƙalilan kaɗai suke yanke shawara a jami'yya ya wuce, kuma na tabbata idan har muka yi wannan yadda ya dace, to ko zamu zama abin misali ga sauran jamiyyu"

To sai dai Jamiyyar ta SPD ta sanya dogon buri a manufofin nata inda daga cikin goman da take hanƙoron ganin sun tabbata, kan gaba shine ƙara mafi ƙarancin albashi zwa euro takwas da centi 50 kowace sa'a da kuma daidaita banbancin kuɗin fenshow tsakanin masu zuwa ritaya a yankin gabashi da yammacin ƙasar. Duk da cewa ana hangen jami'yyar ta CDU zata sassauta a waɗannan fannoni ta fito ƙarara ta ce ba zata yadda masu auren jinsi su iya ɗaukar yara ba, kana ba zata soke wani tallafin da ake baiwa masu yara ƙanana 'yan shekara ɗaya zuwa biyu ba

Haka nan kuma ba kowa ne hankalin shi ya kwanta da wannan ƙawancen da ake ƙoƙarin ƙullawa ba, kamar yadda waɗannan mutanen suka bayyana

ARCHIV - Der SPD-Parteivorsitzende Sigmar Gabriel spricht am 23.05.2013 vor dem Festakt anlässlich des 150. Geburtstages der SPD im Gewandhaus in Leipzig (Sachsen) mit Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU). Rund 200 Sozialdemokraten beraten am 27.09.2013 bei einem Parteikonvent der SPD über die Haltung zu einer möglichen großen Koalition mit CDU/CSU. Es wird damit gerechnet, dass der Vorsitzende Sigmar Gabriel einen Vorschlag für das weitere Vorgehen machen wird. Foto: Kay Nietfeld/dpa (zu dpa "SPD berät bei Konvent über große Koalition" vom 27.09.2013) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Merkel da GabrielHoto: picture-alliance/dpa

Ra'ayoyin al'umma

"Wannan cewa yake yi, a gani na, SPD bata yi nasarar samun gwamnati ba, saboda haka kamata ya yi ta koma ta ci gaba da adawa."

"Wannan kuma cewa yake yi bamu so SPD ta gaza cika alƙawuran da ta yi mana kuma idan har aka yi haɗaka irin wannan dole ne ta mance da wasu abubuwa."

Tsawon lokacin gudanar da wannan yarjejeniya dai zai kasance mai tsawon gaske wanda zai iya kaiwa har lokacin sallar Krisimati kuma idan a cikin yarjejeniyar aka sami wata taƙaddama, komai ma zai iya sauyawa a koma gidan jiya amma kuma shugaban jami'yyar ta SPD Sigmar Gabriel ya ce ya kamata a mayar da hankali kan burin da aka sa a gaba

ARCHIV - ILLUSTRATION - SPD- und CDU-Parteifähnchen vor dem Reichstag in Berlin (Archivfoto vom 20.09.2005, Illustration zum Thema Große Koalition). Foto: Gero Breloer dpa (dpa Serie "Bundestagswahl historisch"; zu dpa "2005: Schröder am Ende - Merkel führt große Koalition" vom 05.09.2013) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: dpa

Matakan kare afkawa cikin matsaloli

"Babu shakka hakan zai iya faruwa wajen yarjejeniya, wato a sami ra'ayoyi mabanbanta, wanda har a ƙarshe su kai ga rashin cimma matsaya, amma kuma idan har mutun ya amince ya shiga tattaunawa, ya kan shiga ne da burin cewa za a cimma nasara ta duk hanyar da ta dace"

Shugabar gwamnatin Jamus na neman jamiyyar da zata yi ƙawance da ita ne bayan da jamiyyar da ta yi haɗaka da ita a baya wato FDP ta gaza dawowa majalisa kuma ana ganin mai yiwuwa su fuskanci ƙarin ƙalubale nan gaba musamman wajen rabon muƙamai domin tun yanzu, jamiyyar SPD na zawarcin mukamin ministan kuɗi wanda ake ganin shi ne a mataki na biyu bayan muƙamin shugabar gwamnati.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu