′Yancin fadin albarkacin baki a Nijer | Siyasa | DW | 05.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yancin fadin albarkacin baki a Nijer

Hukumar sadarwar ta Nijer ta dauki matakin hana saka duk wani gangami ko sanarwar nuna goyon bayan gwamnati daga wasu 'yan jam’iyyun adawa ta kafafen yada labaru mallakar gwamnatin kasar.

Hukumar koli ta sadarwar jamhuriyar Nijer ta yanke hukumcin hana saka duk wani gangami ko sanarwar nuna goyon bayan gwamnati daga wasu bijirarrun yan jam'iyyun adawa keyi a kafafen yada labaru mallakar gwamnatin kasar. A yayin wani taron da hukumar ta gudanar ne dai ta dauki wannan matakin domin hana yawan gangamin yan siyasar da ke ballewa daga jam'iyyun su na adawa suna rankaya zuwa a jam'iyyar dake mulki ko goyon bayanta.

Wannan matakin na zuwa ne a yayin da yan adawa a kasar ke zargin hana su damar shiga kafafen yada labaru mallakar gwamnati, hasali ma sai dai saka kalamai na makiyansu ko ‘ya'yan jam'iyyunsu dake nuna goyon baya ga shugaban kasar.

Matakin da hukumar ta dauka na zuwa ne a yayin da tsami da gurbatar dangantaka suke ci gaba da kamari tsakanin bangarorin dake mulki dama masu adawa inda bayyanar wasu magoya bayan adawar dake tururuwa zuwa nuna goyon bayan su ga shugaban kasa da ma jam'iyyar dake mulki ta PNDS, ke kara harzuka zukatan bangaren jam'iyyun dake adawa wanda dama suka shafe tsawon lokaci suna korafin hana su samun wata dama a cikin kafafen yada labaru mallakar gwamnati domin yada manufofinsu ko akidunsu na siyasa.

Sauti da bidiyo akan labarin