1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Nijar na ci gaba da rike Tchangari

Abdoulaye Mamane Amadou/ Zainab Mohammed AbubakarMay 19, 2015

Jami’an 'yan sanda masu yaki da taddanci sun cafke fitaccen dan gwagwarmayar nan na farar hulla Moussa Tchangari na Kungiyar Alternative tun a ranar Litinin da rana.

https://p.dw.com/p/1FSj3
Moussa Tchangari, Journalist und Menschenrechtler
Hoto: DW/ Thomas Mösch

Kawo yanzu ba wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da abinda ake zarginsa a kai, sai dai lauyan na Moussa Tchnagari ya tabbatar wa DW cewar hukumomi na zarginsa ne da hira a wata kafar yada labaru domin tir da Allah wadarai da kama wasu hakiman yankin Diffa da aka yi.

Da yawa dai na zargin kalamunsa kan yaki da Boko Haram a matsayinsa na dan yankin na daga cikin ababen da suka haifar da kamun nashi. A baya-bayan nan Tchangari ya sha bayyana kallamai na rashin gamsuwa da yanda ake tafiyar da dokar ta baci a Diffa musamman ma batun kwaso jama'ar da ke a tsibirin karamga zuwa doron kasa da hukumomin suka kaddamar.


Da misalin karfe goma sha biyun ranar jiya ne jami'an yan sanda masu yaki da ta'addanci Birgade Anti Terroriste a turance, suka cabke dan gwagwarmayar a yayin da ya isa a harabar ofishin 'yan sandan domin kaiwa wasu hakkimai da aka kama sakamakon zarginsu da rashin kamawa wajan yaki da Boko Haram da hukumomin kasar suka yi tuwo. 'Yan sandan suka dakatar da shi kana kuma suke ci gaba da rike shi zuwa safiyar wannan Talatar.

Soldaten im Niger
Hoto: Desmazes/AFP/Getty Images

Hukumomin dai na zargin Moussa Tchangari ne da yin wata fira a tashar yada labarun kasar Faransa inda ya yi tur da Allah wadarai da kamun da hukumomin tsaron kasar suka yi wa hakiman, kamar yanda lauyansa Me Moussa Koulbaly ya tabbatar.


Bayan ganawa da shi a karon farko lauyan na Moussa Tchangari Me Moussa Koulbaly ya kalubalanci irin yanda hukumomin ke ci gaba da rike Moussa Tchangari sakamakon abin da ya kira 'yancinsa na dan kasa na bayyana albarkacin bakinsa kan abin da ke gudana a cikin kasa.


Duk kokarin da na yi domin jin ta bakin hukumomi akan batun abin yaci tura domin da na tuntubi kakakin rundunar yansanda ta kasa ta waya yaki dauka, kawo yanzu dai babu wani ko wata hukuma da ta fito fili ta ambaci zargi ko tuhumar da take yi wa Moussa. Sai dai takwarorinsa na kare hakkin dan adam sun fitar da wata sanarwa mai kumshe da tir da Allah wadarai da kamun na abokin aikinsu oc


A makwannin da suka gabata dai ne kungiyar ta Alternative Espace Citoyen ta wallafa wani rahoto kan halin da jama'a suke ciki a yankin Diffa da kuma ma batun kwashe dubban mutanen na da kayi a tsibirin karamga, ko ba'idinsa Alternative na yawan kai ziyara da ayyukan wayar da kai ga al'umma a yankin na Diffa abubuwan da ke bai wa kungiyar damar sanin takamaimen halin tagayyara da jama'ar yankin suke ciki wanda ita kuma kungiyar ke wallafawa.