Moussa Tchangari na daya daga cikin fatattun 'yan kungiyoyin fararen hula da ake da su a Jamhuriyar Nijar.
Tchangari ya jima yana gwagwarmaya wajen ganin lamura sun daidaita a Nijar. Alternative Espace Citoyen na daga cikin kungiyoyin fararen hular da ya jagoranta.