'Yan sandan Nijar biyu sun mutu a wani hari
January 24, 2018Talla
Babu karin bayani daga mahukuntan kasar kan harin da kuma sanin ko harin da aka ce an kai a wani kauye mai suna Kokoloukou da ke a yankin Tillaberie na ta'addanci ne a daren Litinin zuwa wayewar garin Talata.
Wani mazaunin kauyen ma ya tabbatar wa kamfanin yada labaran Faransa AFP faruwar lamarin.
A makon da ya gabata sojojin Nijar bakwai ne suka mutu a wani hari da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram da kaiwa. Sai dai kuma yankin da yake fama da ayyukan ta'addancin Boko Haram, a wasu lokuta ma da masu fashi da makami da kan yi garkuwa da manyan 'yan kasuwa don samun kudin fansa.