′Yan sanda na yin bincike a Chemnitz | Labarai | DW | 08.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda na yin bincike a Chemnitz

Jami'an tsaro a Jihar Sachsen-Anhalt da ke a gabashin Jamus sun ce sun gano wasu abubuwa masu fashewa a gidan wani dan gudun hijira na Siriya.

Yanzu haka dai 'yan sandar na ci gaba da yin bincike domin samun mutumin wanda ya ranta cikin na kare,Tom Bernhardt shi ne kakakin 'yan sandar na jihar.''Mun bincika gidansa da kuma gewaye,mun samu wasu abubuwan masu fashewa, amma dai bincike ne kawai zai iya tabbatar da cewar ko abubuwan an hadasu  ne don kai hare-haren.''