′Yan sanda a Jamus sun kafa shingen kankare a gaban babbar majami′ar birnin Kwalan | Labarai | DW | 23.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda a Jamus sun kafa shingen kankare a gaban babbar majami'ar birnin Kwalan

An dai tsaurara matakan tsaro a birane da dama na Jamus tun bayan harin nan da aka kai da mota da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13 a birnin Barcelona a makon da ya gabata.

Symbobild Polizei Köln (picture-alliance/dpa/J. Knoff)

'Yan sanda a gaban majami'ar birnin Kwalan

'Yan sanda a Jamus sun kafa shingayen kankare a gaban babbar majami'ar birnin Kwalan mai dadadden tarihi, bayan da rahotanni suka ce masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci na da nufin kai hari kan wani muhimmin wuri na tarihi biyo bayan harin da aka kai kan majami'ar La Sagrada Familia ta birnin Barcelona da ke kasar Spaniya.

An dai tsaurara matakan tsaro a birane da dama na Jamus tun bayan harin nan da aka kai da mota da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13 a birnin Barcelona a makon da ya gabata.

Da farko dai mahukunta a Jamus sun yi dari-darin kakkafa shingayen bincike a gaban wuraren tarihi bisa fargabar cewa hakan zai hana masu yawon buden ido kai ziyara a wadannan wurare.