1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yaudari 'yan Najeriya zuwa Rasha

Mohammad Nasiru Awal YB
July 10, 2018

Tare da yi musu alkawarin zama kwararrun 'yan wasan kwallon kafa a manyan kungiyoyi, masu fataucin dan Adam sun yaudari daruruwan 'yan Najeriya zuwa kasar Rasha.

https://p.dw.com/p/319td
Russland Nigerianer in Moskau | NGO "Alternative"
Hoto: DW/M. Soric

Da isa kasar ta Rasha dukkan fatan da suke da shi ya gushe, inda suka tsinci kansu cikin hali na tsaka mai wuya a birnin Mosko. Wasu 'yan Najeriya 'yan uwa juna masu shekarun haihuwa tsakanin 20 zuwa 25 an yaudare su zuwa kasar Rasha da fata na bogi na zama kwararrun 'yan kwallon kafa. Saboda kunya sun sakaya sunansu. Tun a birnin Legas wasu 'yan Najeriya suka tinkare su da cewa ko da burinsu na zama kwararrun 'yan kwallon kafa bai cika ba, za su iya samun aiki mai kyau a Rasha cikin sauki. Kasacewa karaminsu na wasan kwallo a Najeriya, sun yi fatan likkafarsu za ta yi gaba a Rasha.

Sun dai shiga Rasha ne da wata takardar tafiya da ake kira FAN-IDs, wadda gwamnatin Rasha ta ba wa baki da ke halartar gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya. Ta kunshi dukkan bayanan da ake bukata na matafiyi kuma ta maye gurbin biza a tsawon lokacin gasar.

Sai dai daga saukarsu birnin Mosko, 'yan uwan junan suka gane cewa an yaudare su, domin lambar wayar da aka ba su ba ta aiki. Ba a yi kwana uku ba kudin hannunsu ya kare suka fara kwana a masallaci da filin Allah ta'ala. Sun tuntubi ofishin jakadancin Najeriya a Mosko, maimakon tallafi, sai aka ba su lambar wata kungiyar agaji mai zaman kanta mai suna Alternativa, kamar yadda daya daga cikinsu ya nunar:

 "Daga Najeriya na zo in kalli gasar cin kofin duniya. Kudina ya kare ba zan iya biyan kudin otel ba, ina son in koma gida. Na tafi ofishin jakadancin Najeriya, sun tura ni wajen kungiyar agaji ta Alternativa, wadda ta ba ni wurin kwana har zuwa lokacin da zan koma gida. Kasancewa ni dan Najeriya kuma na nemi taimako daga ofishin jakadancinmu, amma ban samu taimakon ba, gaskiya na ji haushi."

Russland WM 2018 l Nigeria vs Island - Fan
'Yan Najeriya da dama sun je kallon wasan na duniyaHoto: Reuters/J. Silva

Wakilin DW a birnin Mosko ya tuntubi ofishin jakadancin Najeriya don jin gaskiyar labarin, inda babban jami'in kula da sashen ilimi da al'adu da watsa labarai, Olumide Folarin Ajayi ya ce suna da labarin 'yan Najeriya da suka shiga halin ni 'ya su a Rasha bayan an yaudare su zuwa kasar. Ya ce a shirye ofishin jakadancin yake da ya taimakawa duk dan Najeriya da ya nemi taimakonsa. Amma kuma ya kara da cewa tun farko hukumar yaki da fataucin mutane a Najeriya ta gargadi 'yan kasar da su yi hattara da mayaudara da za su yi amfani da gasar cin kofin duniya don yi wa mutane zamba:

Russland WM 2018 l Nigeria vs Island
Najeriya dai bata yi rawar gani ba a gasar ta RashaHoto: Reuters/U. Marcelino

"A iya sanina hukumar yaki da fataucin mutane wato NAPTIP ta yi ta jan hankalin 'yan Najeriya da su yi hattara da mayaudara da za su yi amfani da sassaucin izinin shiga Rasha lokacin gasar cin kofin duniya, wadanda za su yi musu alkawuran karya cewa za su sa rayuwarsu ta inganta a Rasha."

DW ta tuntubi ofishin hukumar ta NAPTIP a Abuja don tabbatarwa ko ta fitar da wannan gargadi, amma ofishin ya ce sai an rubuto wasika a hukumance. Daga ranar 23 ga watan na Yuli izinin zama a Rashar zai kare. Yanzu haka dai daruruwan 'yan Najeriya na watangaririya a Rasha.