1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru ta tabbatar da mutuwar 'yan kasar a yakin Ukraine

Zakari Sadou ZMA
April 9, 2026

Tuni mahukuntan Kamarun suka wallafa sunaye da kuma bayanan waɗanda suka rasa rayukansu a yaƙin bayan da suka tafi Rasha bisa kashin kansu.

https://p.dw.com/p/5BwJy
Hoto: REUTERS

Kamaru ta ce hukumomin Rasha sun tabbatar da mutuwar 'yan Kamaru 16 da ke fafatawa da Ukraine, wannan shi ne karo na farko da kasar Afirka ta Tsakiya ta yi magana game da shigar 'yan kasarta cikin yaƙin da ake ci gaba da yi.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Litinin 6 ga Afrilun shekarar 2026, ma'aikatar harkokin wajen Kamaru ta yi kira ga iyalan waɗanda suka mutu da su tuntubi jami'an ma'aikatar a Yaounde babban birnin ƙasar.

A halin da ake ciki, wata sanarwa da ke ƙunshe a cikin takardar diflomasiyyar ba ta bayyana yadda mutanen 16 suka ƙuduri aniyar shigar wa Rasha yaƙin ba, haka kuma ba su bayar da cikakken bayani kan wurin da aka kashe su da lokacin da suka mutu ba.

A wani ɓangare kuma tun a watan Fabrairu binciken kungiyar All Eyes on Wagner ta malaman jami'a da kuma kwararru kan tsaro a yanar gizo  ta bayyana cewa yan Kamaru sama da dubi 1,700 dake taimakawa Rasha a yaƙin da take fafatawa da Ukarine, wadda tace adadin na iya zarta hakan.

Frankreich Paris 2019 | Kameruns Präsident Paul Biya beim Pariser Friedensforum
Hoto: Charles Platiau/REUTERS

A yayin da Rashar ta musanta zargin da aka yi mata cewar ta ɗauki 'ƴan Afirka don su agaza mata a yaƙin da take gwabzawa da Ukraine, inda ta ce zancen bashi da tushe balle makama.

A nata ɓangaren, Kamarun ta ce bata tura dakarun soji zuwa wata ƙasa don su yi yaƙi a hukumance ba, tare da gargaɗi ga 'ƴan ƙasar da su kiyayi duk wata ɗabi'a ta yin hakan saboda rashin alfanunsa.

Paul Stéphane Menounga masanin harkokin siyasar Kamaru ya bayyana takaicinsa kan rashin iya amfani da diflomasiya wajen warware wasu matsaloli tsakanin kasa da kasa yayin da ake samun sojojin Kamaru da ke barin aiki domin shiga aikin sojan haya a Rasha saboda rashin isasshen albashi.

"A gaskiya wannan hujja ce da ke nuna cewa diflomasiyar Kamaru ta gaza, ina da wani wanda yake tamkar kani ne a waje na, yana daga cikin wadanda suka mutu, ya kasance jandarma, ya bar aiki saboda yayi imanin cewa yanayin rayuwa idan aka kwatanta da albashin da suke samu, ya bar aikin soji domin an yi masa tayi mafi kyau a Rasha sai ya shiga yaki tsakanin Rasha da Ukraine ya mutu yau watanni biyu Kamaru ta gaza”

DW ta tuntubi iyayen yaran da suka mutu a yakin Rasha da Ukraine amma sun bukaci da a sakaye sunayensu, sun yi kira ga hukumomin Kamaru da su yi kokarin maido musu da gawarwakin, domin yi musu zaman makoki cikin mutunci kamar yadda al'adun Kamaru ke bukata

"Gwamnatin Kamaru da ke kula da 'yan kasarta a kasashen waje su maida mana da gawarwakinsu, mu 'yan Kamaru ne musamman ma 'yan Bantou bama iya zaman makoki ba tare da gawa ba”.

Wadannan iyayen matasan du suka sadaukar da rayuwarsu domin kare kasar da ba tasu ba, ya jefa su cikin mummunar hali sun kasance cikin bakin ciki. Galibin matasan ba su cika shekaru 29 ba, sun bar Kamaru saboda kara ilimin na'urar kwanfuta, bayan 'yan shekaru ba a sake jin labarinsu ba, bayan kwashe watanni bakwai ana nemansu.

Russland Moskau 2026 | Wladimir Putin empfängt Ägyptens Außenminister Badr Abdelatty
Hoto: Alexander Zemlianichenko/AP Photo/picture alliance

"Yaro na, ya tafi yayin da yake jami'a, ya tafi ne na kara ilimi, bayan haka ya shiga aikin sojin Rasha yana da ilimin kwanfuta mun samu wannan labari a watan Afrilun 2025, cewa an dauke shi aikin soji a Rasha amma tun watan Mayu 2025, bamu sake jin labarinsa ba, mun yi bincike wajen 'yan Kamaru mazauna Rasha suka sanar damu a watan Disamba 2025 cewa duk tsawon watanni bakwai ba tare da wani labari ba ya nuna alamu akwai lauje cikin nadi”

Abin damuwa a nan Kamaru ce ke da matasa mafiya yawan wadanda suka rasa rayukansu da mutum 94  kusan kaso 28 na yan Kamaru da aka gano sun mutu ko suka ji rauni ko kuma suke tsare inji binciken kungiyar All Eyes on Wagner.

Dw ta nemi tattauna da daya daga cikin ma'aikacin harkokin kasashen waje a Kamaru domin bayani akan matakin da su dauka domin yaki da masu rejistan sunayen mutanen wadanda suke bas u damar shiga aikin sojin hakan ya ci tura