′Yan gudun hijira sun tsallake kogi daga Girka zuwa Macedoniya | Labarai | DW | 14.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan gudun hijira sun tsallake kogi daga Girka zuwa Macedoniya

Bayan zama na kwanaki cikin mawuyacin hali a kan iyakar Girka da Macedoniya, 'yan gudun hijirar sun doshi kasar Macedoniya.

Daruruwan 'yan gudun hijira da bakin haure da suka makale a Girka sun fara tsallakewa zuwa makwabciyar kasa Macedoniya, suna fatali da rufe kan iyakokin da kasashen yankin Balkan suka yi. Daruruwan mutane dai sun doshi kan iyakar bayan kwashe sa'o'i suna tafiya cikin ruwan sama kamar da bakin kwarya. Wasunsu kuma sun ketara wani kogi rike da yara. 'Yan gudun hijirar sun gano wata kofa a shingen kan iyaka da ke kusa da wani kauye a Girka, inda daga nan suka kutsa cikin Macedoniya. Masu aikin agaji na kasa da kasa da kuma na kasar Girka su suka rika taimaka wa 'yan gudun hijirar tsallake kogin. Wannan dan Siriya da ya ce sunansa Yusuf cewa ya yi.

"Na doshi wurin da mutane suka dosa, wato kasar Macedoniya. Da wannan safiyar 'yan sandan Macedoniya ba su bude kan iyakar ba, hakan ya janyo babbar matsala. Mutane na son su je Macedoniya da kuma Jamus."